AHMAD MANASRA
Wannan shine ahmad wanda israel suka kama suka kulle shi a gidan yari tun yana shekara 13
Gashi zuwa yanzu yakai shekara 21 yana gidan yari
Ga labarin yadda aka kamashi;
Ahmad da dan uwansa hassan me shekara 15 ana zarginsu da kashe yan kasan israel mutum biyu a wata unguwa a yankin jerusselam, a nan take wasu yan kasar israel suka harbi hassan har lahira shi kuma suka masa duka suka suka bishi da mota suka bigeshi,
A anan ne kan sa ya bugu kuma ya fara zubar da jini, bayan anyi binciki aka gano ya samu karayar a qashin sa na kwakwalwa,
Daga nan yan sandan israel suka tafi tashi suka tsare, a lokacin yana shekara 13 kuma israel ta fitar da doka bazatayiwa yaron kasa da shekara 14 hukunci ba,
Hakan ya saka aka ajiye yaron a hannu seda yakai shekara 14, daga nan kotu yanke masa shekara 12, a shekarar 2016
kotun israel tana zargin ahmad da kisan kai.
A shekarar 2021 a watan december aka bawa wani likita izini da yaje ya duba Ahmad, bayan likitan ya duba Ahmad ya tabbatar da ahmad ya samu tabin hankali bayan wannan bigeshi da mota da mazauna israel sukayi.
A shekarar da ta wuce 2022 israel ta fitar da sanarwar wanke ahmad daga zargin kisan kai, kuma da za a duba yiyuwar sakin shi,
Amma har zuwa yau ba su sakeshi yana tsare a gidan yari a kasar israel kuma fa shi ba dan kasar bane.
Wannan labarin ya inganta daga al jazeera zaka iya bibiya domin tabbatarwa
0 Comments