Abubuwa Biyar Da Musulmi ne suka fara Yinsu a Duniya
Hakika duniyar wannan zamani ta sha bam bam da duniyar shekaru 1000 da suka wuce, a wannan zamanin muna cike da abubuwa na cigaba masu yawa kamar su; Jirgin sama, Camera, wayar hannu da dai sauransu, amma ko ka san dayawa daga abubuwan da muke gani a yanzu na cigaba an fara kir-kirar su ne shekaru dubu da suka wuce, wasun su ma musulmi ne suka fara ki-kirar wadannan abubuwa, ku biyomu domin karanta kadan daga ciki.
1. Jirgin Sama( air plane ). An samo Asalin basirar yin sama ne daga kokari na wani babban masani kimiyya musulmi tun shekara ta 800 me suna ABBAS IBN FIRNAS, shine yayi tunani ya za ayi mutum ya tashi sama kamar tsuntsu, se yayi amfani da basirar da Allah ya bashi har ya gwada tashi sama, daga nan aka samo asalin jirgin sama
2. Asibiti (Hospita). Asalin fara gina wuri domin kula da marasa lafiya da basu magani,
Wannan ma ya samo asali daga wani malamin musulunci me Suna AHMAD BN TULUN a shekara 872 a garin cairo a kasar misrah, a lokacin da wannan malami ya bude wannan waje yana kula da marasa lafiya da basu magani kyauta, daga wannan dabara ta wannan malami se asibiti ya watsu a sassaan duniya
3. ToothBrush ( magogin hakora). Hakika abinda tariha yazo mana dashi shine Asalin goge baki. Shine manzon Allah shine ya Shahara da amfani da itace wajen goge baki a tarihi, yana amfani da itacen bishiyar (miswak tree) shine muke cewa ASUWAKI, wanda har ya sunnan tar da haka ga musulmi da sun dinga goge hakoran su kafin kowace sallah
4. Surgery (tiyata). Ko ka san ana yin tiyata Shekara 1000 da suka wuce, babban malamin musulunci me suna AL-ZAHRAWI, ya wallafa wani rubutu da yakai shafi 1,500 inda a ciki yayi duk bayanin yadda ake tiyata, turawa suna amfani da wannan littafin a matsayin bincike da hujja akan harkar Surgery, kuma shine ya kir-kirar abinda za ayi amfani dashi wajen dinke rauni
5. University (jami'a). Harkar bada ilimi harka ce me muhimmanci a duniya, to shima musulmi ne suka fara kir-kirar karatun jami'a, abinda tarihi yazo mana dashi shine, jami'a ta farko a duniya ita ce jami'ar qarawiyin (University of Qaraawiyin) dake kasar morocco a shekara 859, a wannan jami'a an fara yin ta ne a masallaci inda ake amfani da limamai wajen koyar da dalibai ilimi na wasu shekaru, fannoni daban daban na addini.
Bayan kammala wannan shekaru ana bawa dalibai shedar kammala karatu wato (ijaza) a matsayin shaidar degree, to daga nan aka samo Asalin fara University a duniya
Ku cigaba da bibiyar mu domin samun tarihi ingantacce
Domin bibiyar Tushen labari
0 Comments